Lamborghini Huracán LP 610-4 t
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Fassarar littafin
*** Usulus sunnah ***
Na
Imam Ahmad Bin Hambal
Shirin da dan uwanku
Abu Jareer Ameer bn Hamza Zakigold
Yake GabatarwaKuna iya binsa ta face book
Wanda ya tsara kuma ya shirya
Basheer journalist sharfadi (Abu Hafsat)
A sha karatu lapiya

FASSARAN USULUS SUNNAH NA IMAM AHMAD BIN HANBALI
.
Darasina 1
.
Dasunan ALLAH mai Rahma maijin Kai, tsira da aminci sukara tabbata ga shugaban duk wani Ahlussunnah, abin kaunarsa kuma abin koyinsa Annabi Muhammad s.a.w da iyalan gidansa da almajiransa da duk wanda yabiyo bayansu da kyautatawa.
.
bayan haka muna fatan ALLAH ya daidaita tinaninmu da fahimtarmu ya datar damu gaskiya kuma ya bamu ikon aiki da abinda zamu karanta.
.
Mallam yace:- Abdus dan Malik ya labartamin cewa: yaji baban Abdullah wato Ahmad dan Muhammad dan Hanbali(ALLAH yamasa Rahma) yanacewa:-
.
Asali/ginshikai na Sunnah awajenmu:
.
1-Riko da/Bin abinda sahabban manzon ALLAH s.a.w suke kai(cikin addini)
.
2-Yin koyi dasu(sahabbai). kenan duk mai daawar shi Ahlussunnahne to muganshi yana koyi da sahabban Annabinmu s.a.w.
.
3-Barin aikata bidi'ah(kowace irice).
.
4-Dukkanin bidi'a batace.kai Alhamdulillah ashe karyane kawai akema shehul Islam na cewa wai shine yafara daurama dalibai fahimtar hakan.
.
5-Barin husuma dakuma zama tareda ma'abota son rai(yan bidi'a).
.
6- Barin Jayayya, kace nace, musu cikin Addini (kalubale gareku yan uwana Ahlussunnah).
.
.
zamu kwana anan sai in ALLAH yakaimu darasi nagaba.
.
.
FADAKARWA: Isnadin da muka kawo na wannan littafin ba shikai bane mun zabeshine kawai don takaita Rubutu, amma wannan Littafi an ruwaitotane ta hanyoyi tara, maison dubawa saiya nemi bugun Maktabatu ibn Taimiyya wanda ke Misra, tahqiqin Walid bin Saif Annasr.
.
.
Sannan duk wanda yaga gyara ko karin bayani zai iya tuntubana ta:-
.
hamzaameer236@gmail.­com,
hamzaameer708@gmail.­com,
zakigold16@ yahoo.com
.
.
Ko kayi mana comment ta nan


FASSARAN USULUS SUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI
.
Wanda dan uwanku Abu Jareer Ameer bn Hamza Zakigold yake gabatarwa
.
Darasina Biyu:2
.
Dasunan ALLAH mai Rahma maijin Kai, tsira da aminci sukara tabbata ga shugaban duk wani Ahlussunnah, abin kaunarsa kuma abin koyinsa Annabi Muhammad s.a.w da iyalan gidansa da almajiransa da duk wanda yabiyo bayansu da kyautatawa.
.
bayan haka
.
muna fatan ALLAH ya daidaita tinaninmu da fahimtarmu ya datar damu gaskiya kuma ya bamu ikon aiki da abinda zamu karanta.
.
Inbamu mantaba wancan makon daya gabata mun tsayane agaba ta shida yau zamu tashi ana Bakwai, Mallam yace:
.
7-Sunnah awajenmu: sune Hadisan Annabi s.a.w.
.
8-kuma su Hadisan suna fassara Qur'ani, domin sudin dalilaine/hujjojine na alqur'ani..
.
9-Babu kiyasi cikin sunnah. anan wurin sunnah yana nufin Tauhidine ba rassa na fiqhuba kamar yanda Shehul Fauzan a fassara irin wannan gaba a Sharhus sunnah na Imamul Barbahari, haka shima Sheikh Ahmad dan Yahaya Annajami ya fassara wannan gaba a littafinsa
"Irshadu sari fi sharhu sunnah lilbarbahari".
.
10-Ita Sunnah(Tauhidi/­aqida) baa buga mata misali(wato bada misalai ake tabbatar da itaba), baa riskanta da hankali ko son rai(ba kawai abinda yai dai-dai da hankalinka shine zaka yarda dashiba), ita Sunnah ba wata aikine saboba face bi(wato bin Qur'ani da Hadisan Annabi s.a.w bisa fahimtar sahabbansa da wadanda suka biyo tafarki irintasu) da barin son zuciya.
.
.
zamu kwana anan, sai in ALLAH yabamu aron rai zuwa darasi na gaba,
.
ya ALLAH ka kara Tsira Aminci Ni'ima ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w
.
Via:- Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa
.
https://­m.facebook.com/­HaqqinAllahAkanBayins­a


FASSARAN USULUSSUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI
.
Darasi na uku
.
11-Mallam yace: yana daga cikin Sunnoni wajibai wadanda duk wanda yabar wani abu daga ciki(bai yarda dashiba), kuma baiyi imani dashiba, to wannan ba Ahlussunnah bane(sune tindaga gaba na 12 harzuwa na 50):
.
12-Imani da kaddara na alhairi kona sharri, da gasgata Hadisanda suke bayani gameda Kaddaran, da sallama mata/yarda da ita, kuma kada kace: don me?(misali donme Allah ya halicci kaza da kaza?), kuma kada kace: ya akayi? abinda ake bukata kawai gasgatawa dakuma imani da ita(Kaddaran). Duk wanda baisan fassaran Hadisiba amma malamai sukamasa bayani ta littafan fiqhu to wannan ya isheshi kuma za'amar hukunci da abinda ya karanta, dolene yayi Imani da Hadisin dakuma duk abinda ya kunsa kuma ya Sallamawa bayanin magabata akai, misali: Hadisin(Ibn Mas'ud radiyallahu anhu, da Annabi s.a.w yakecewa: lallai dayanku ana tattara halittansa cikin cikin mahaifiyarsa kwana arba'in yana maniyi, harzuwa karken hadisin duba Buhari(3208) da Muslim(2643) da dai sauran Hadisanda suke magana akan kaddara da Hadisanda suke magana gameda ganin Allah dukkansu dana Sunayen Allah dolene ayi Imani dasu kuma kada ayi musun koda harafi daya rak acikin duk Hadisin dayazo gameda hakan ta hanyar Amintattu.
.
kuma kada kayi jayayya da kowa cikin lamarin kaddara hakama kada kayi gogaiyya da kowa, kuma kada ka koyi musu domin musu gameda Kaddara da Kur'ani da makamantansu suna daga ababen ki wadanda aka hana, duk mai aikata haka baya dacewa da Sunnah idan kuma ya dace da Sunnah to dole saiyabar musu da jayayya ya sallama kuma ya yarda da duk ababenda suka inganta.
.
zamu kwana anan, sai in ALLAH yabamu aron rai zuwa darasi na gaba,
.
ya ALLAH ka kara Tsira Aminci Ni'ima ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w
.
Via:- Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa https://­m.facebook.com/­HaqqinAllahAkanBayins­a


FASSARAN USULUSSUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI

.Darasi na Hudu

13-Alkur'ani maganan ALLAHne ba halittansa bane, bawani abune saboba don ance Kur'ani ba hallitta bane, mallam yace: domin shi maganar ALLAH(Kur'ani) babu wani abu aciki daya nuna cewa Kur'ani halittane, ballantana daman ba halittan bane.

Ahir dinku daduk wanda ya kirkira magana ya jinginama Kur'ani koda da lafazine(kalma daya tak) ko makamancin hakan, duk wanda ya tsaya musu gameda Kur'ani yace: bansaniba halittane koba halittaba, ammadai maganan ALLAHne to wannan shima dan Bidi'ane, dai-dai yake da wanda yace: Kur'ani halittane.

Abin sanidai Kur'ani maganan ALLAHne ba halittansaba.

zamu kwana nan, sai in ALLAH yabamu aron rai zuwa darasi na gaba,

ya ALLAH ka kara Tsira da Aminci Ni'ima ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w

Via:- Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa https://­m.facebook.com/­HaqqinAllahAkanBayins­a


FASSARAN USULUSSUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI
.
.Darasi na Biyar
.
14:-Ahlussunnah sunyi Imani za aga Allah ranar Alkiyama kamar yanda yazo a Hadisai ingantattu.
15:- kuma lallai Annabi s.a.w yaga ubangijinsa, haka aka ruwaito daga Annabi s.a.w ta hanya ingantacciya, Qatada ya ruwaito daga Ikrama daga dan Abbas, dakuma Hakamu ta hanyar Aban daga Ikrama daga dan Abbas. Haka shima Aliyu bin Zaid ya ruwaito daga Yusuf dan Mihran, daga dan Abbas. Hadisin awajenmu yananan a bisa zahirinsa kamar yanda yazo daga Annabi s.a.w, magana game dashi(Hadisin) Bidi'ane, sai dai mu munyi Imanine dashi azahirin yanda hadisin yazo bama gogaiya dakowa cikin hakan.
.
FADAKARWA GAMEDA WANNAN GABAN NA SHABIYAR
Anan mallam yana nufin Annabi s.a.w yaga Ubangijine da zuciyarsa bada Idanunsaba, saboda babu wani baya dazai iya ganin ubangijinsa anan Duniya sai dai inya mutu kamar yanda Annabi s.a.w yafada: (ku sani babu wani cikinku dazaiga Ubangijinsa har sai inya mutu), kamar yanda shima Annabin s.a.w baiga Allahba da idanunsa kamar yanda Abu zar ya tambayeshi sai yace: (Haske nagani) awata ruwayar kuma yace Haskene nagani. Dukkanin Hadisan Imam Muslim ya ruwaitosu, atakaice dai baa ganin Allah aduniya sai a Lahira amma akan iya ganinsa cikin Mafarki kamar yanda Annabi s.a.w yabada labari amma ganinsa a Duniya a farke bashi yiwuwa sai a Lahira kamar yanda Hadisai suka nuna Muminai zasu gansa hakama yan Aljanna acikin Aljanna, wannan shine Ijimain Ahlussunnah wal Jamaa.
.
zamu kwana nan, sai in ALLAH yabamu aron rai zuwa darasi na gaba,
.
ya ALLAH ka kara Tsira da Aminci Ni'ima ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w
.
Via:- Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa https://­m.facebook.com/­HaqqinAllahAkanBayins­a


FASSARAN USULUSSUNNAH NA IMAM AHMAD
DAN HANBALI
.
Darasi na shida
.
Mallam yaci gaba da jero mana Aqidun Ahlussunnah kamar haka:
.
16- Duk Ahlussunnah waljamaah sunyi Imani da zaa auna aiyukan bayi ranar Kiyama, kamar yadda Hadisi ya tabbata Annabi s.a.w yace za'a auna aikinbawa ranar kiyama, saikaga ko nauyin fiffiken saura aikin bai kaiba. Buhari
4729, Muslim 2785. Kamar dai yanda ya tabbata a Hadisai da dama, Mallam yace Imani
da hakan wajibine da yarda dahakan, da kaucema duk wani wanda yai musun hakan,
da barin jayayya dashi duk wajibine.
17- Kuma lallai Allah madaukakin sarki zaiyi magana da Bayinsa ranar kiyama batare da wani mai fassaraba a tsakani, munyi Imani
kuma mun gasgata hakan.
18-Munyi Imani da tafkin alkausara, lallai Annabi s.a.w yana tafki ta musamman aranar
kiyama zaa bijiro da al-ummansa zuwaga tafkin, fadinsa tafiyan wata gudane hakama tsawonsa, yanada kwazazzabai kamar adadin taurarin sama kamar yadda Hadisai ingantattu suka tabbatar ta hanyoyi masu yawa.
.
zamu kwana nan, sai in ALLAH yabamu aron rai zuwa darasi na gaba,
.
ya ALLAH ka kara Tsira da Aminci Ni'ima ga
shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w
.
Kuziyarcemu ashafinmu mai suna Haqqin
.
ALLAH AKAN Bayinsa https://m.facebook.com/­HaqqinAllahAkanBayinsa


FASSARAN LITTAFIN USULUS SUNNAH NA IMAMU AHMAD DAN HANBALI
.
Bugun Maktabatu Ibn Taimiyyah dake Misra.
.
Daga shafin Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa
.
Darasi na bakwai
.
Mallam yacigaba da jero mana Akidu na Ahlussunnah wadanda suke yarda dasu wajibine kuma duk wanda yayi musu ko yaki wani abu daga ciki toba Ahlussunnah bane, mallam yajera mana gabobi goma sha takwas a baya yanxu zamu tashi ana sha tara.
.
19-Yin Imani da Azabar kabari.
.
20- Lallai wannan Al-umma ta Annabi s.a.w zaa fitineta acikin kabarinta, zaa mata tambaya danganeda Imani, da Muslunci, dakuma waye Ubangijinta? Dakuma waye Annabinta? Munkarun da Nakirun zasu zo ta yadda Allah s.w yaso dakuma yanda yanufa, imani da gasgata hakan wajibine ga duk wani Ahlussunnah.
.
Zan dakata anan sai nasake samun lokaci, danna wannan blue din kai like din page dinmu Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­


FASSARAN LITTAFIN USULUS SUNNAH NA IMAMU AHMAD DAN HANBALI
.
Bugun Maktabatu Ibn Taimiyyah dake Misra.
.
Darasi na Takwas

adarasinmu na baya mun tsaya a gaba na Ashirin cikin jeren Akidu na Ahlussunnah wal jamaah wadanda suke dolene yin Imani dasu dakuma gasgatasu kuma duk wanda kaga yana MUSUN dayansu toba Ahlussunnah bane, yau zamu tashi a gaba na Ashirin da daya
.
21- YIN IMANI DA CETON ANNABI S.A.W,dakuma cetonsa ga wasu Mutane da za'a fitar dasu daga Wuta bayan sun konu sun zama Toka, yayinda za'a Umurcesu zuwa wata korama a Kofar Aljannah kamar yadda ya tabbata a Hadisi, ta yanda Allah kuma yaga dama, mudai munyi Imani kuma mun gasgata.
.
22- Dayin Imani cewa Dajjal mai shafaffen Albarka zai fito, an rubuta a tsakanin Idanuwansa KAFIRUN, kamar yanda Hadisai suka tabbar, dolene yin Imani cewa hakan zai faru.
.
23- Kuma lallai Annabi Isa dan Maryam s.a.w zai sauko(daga sama) yakashe Dujjal a kofar Luddin.
.
Zamuci gaba da yardan ALLAH da Amincewarsa
.
ku ziyarcemu a wannan shafin:
Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­
Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­
Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­
Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­
Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­ Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­ Haqqin ALLAH AKAN Bayinsa­


FASSARAN LITTAFIN USULUS SUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI
.
Bugun Maktabatu Ibni Taimiyya dake Misra
,
DARASI NA TARA//009
,
Inbamu mantaba a darasi na takwas mun tsayane a gaba 23 cikin jerin Aqidun Ahlussunnah wadanda suke dolene yin Imani dasu, yau zamu tashi ana 24.
.
24- Imani furucine da akeyi da Baki dakuma Aiki na gabobi, Imani yana raguwa yana karuwa, kamar yanda Hadisi ya tabbata Annabi s.a.w yace: ((Mumininda Imaninsa yacika shine wanda yake kyautata dabi'a)) Sahihul Jami'i 1230.
.
25-Duk wanda yabar Sallah hakika tabbas ya kafirta, babu wani aiki wanda barinsa kafircine bayan Sallah, duk wanda yabarta kafirine, hakika Allah ya halasta kasheshi.
.
Zamu tsaya haka sai darassi na gaba in Allah ya bamu aron rai, subhanallahumma wabihamdika ashhadu anlailaha illa huwa astagfiruka waatubu ilaik,


FASSARAR USULUS SUNNAH NA IMAMU AHMAD BIN HANBAL
DARASI NA //10

A yau zamu tashi agaba na ashirin da shida kicin aqidun ahlussunnah wadanda imani dasu wajibine.

26: Mafificin wannan Al-ummah bayan Annabinta shine Abubakar sadiq, sannan UMARU dan Haddabi sannan Usman dan Affan, Imam Ahmad hace muna gabatarda wadannan ukunne Kalmar yadda SAHABBAN ANNABI S.A.W suka gabatar dasu, basuyi savaniba.
Sannan bay an wadannan ukun, Ashabu shura su Bihar: Aliyu dan Abi Dalib, da Dalha, Zubair, da Abdulrahman dan Auf, da Sa'ad, dukkanninsu sun can canci Halifanci, kuma dukkaninsu jagororine.

Mina hujjane da Hadisin dan Umar(mun kasance muna kididdigewa alhalin Annabi s.a.w yana Raye kuma sahabbansa suna Raye, muna cewa Abubakar sannan Umar sannan Usman, said muyi shiru). Cuba musnad hadisi na 4612, Buhari 3655.

Sannan bayan Ashabus shura: wadanda suka halarci yakin Bandar cikin muhajirai, sannan wadanda suka halarci Bandar cikin mutanen madina cikin sahabbab Annabi s.a.w qwarqwadon hijira dakuma wadanda suka rigayi, mataki-mataki.

27:Sannan mafifitan mutane bayan wadannan sune: sahabban Annabi s.a.w wadanda aka aikoshi acikinsu, Wanda ya tattara dukwani Wanda ya zauna dashI name tsawon shekara ko wata days, ko yini guda ko awa guda koya ganshi yana mai Imani dashi to yana saga cikin sahabbansa, dukkanin wadannan sahabbaine kowanne gwargwadon zamansa da Annabi s.a.w da gwargwadon yanda yaji daga gareshi dakuma yanda ya ganshi.

mafi kasa kasa amatsayi cikin sahabbai yafi duk wata al-umma da bataga Annabiba falala koda wannan al-umma tazo da duck wani aiki na alhairi.

Alhamdulillah ya Allah kabamu ikon koyi dasu


FASSARAN LITTAFIN USULUS SUNNAH NA IMAM AHMAD DAN HANBALI

Darasi na //011

A darasi na goma mun tsayane a gaba na ashirin da bakwai ciki jerin akidoji dasuka zama wajibi gaduk wani Ahlussunnah yai imani dasu kuma ya yardu dasu Kalmar yanda Imamu Ahlussunnati waljamaa ya ambata, agurguje zamu tashi gaba na 28.

28-Da sauraro tareda biyayya ga jagorori dakuma shugaba acikin addini,wannan shugaban yakasance mai yima Allah biyayyane koko mai bijirema dokokinsane, Halifaneshi da jamaa suka zaba suka yarda dashi koko juyin mulki yayi yake mulkansu da karfin tuwo, yimasa biyayya wajibine.

29-Kai hari da yake-yake tareda shuwagabanni na Addini yananan har tashin kiyama akan Mumini da fajiri-baa dainawa.

Ya Allah kasanyamu cikin Ahlussunnah wall jamaa kabamu ikon aiki da sunnah, Amiin



Koma saman shafi

→Labarai
1234...9899100»

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 210677

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358